BBC navigation

Neymar yace lokacinsa na wasa a Turai bai yi ba

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 21:08 GMT
neymar

Neymar

Matashin dan wasan nan na Brazil Neymar ya takawa kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Turai da ke faman zawarcinsa birki inda ya ce lokacinsa na kaura daga kasarsa Brazil, zuwa Turai ya yi kwallo bai yi ba.

Dan wasan wanda ke tashe a fagen wasan a Brazil da Latin Amurka, yanzu ya ce, duk da cewa burinsa ne ya yi wasa a Turai, to amma yanzu lokaci bai yi ba da zai tafi wannan cirani.

Dan wasan gaban wanda ya sami lambar azurfa da kungiyar wasan Brazil a gasar Olympics ta London 2012, a na ganin manyan kungiyoyin kasashen Turai na zawarcinsa ganin yadda tauraruwarsa ke haskakawa yanzu a Latin Amurka.

Dan wasan mai shekaru 20 ya taimakawa kungiyarsa ta Santos ta dauki kofin kwallon kafa da ya fi kowanne armashi a Latin Amurka, Copa Libertadores a 2011, karon farko da kungiyar ta dauki kofin tun bayan da tsohon gwanin dan wasan kwallon kafa na duniya Pele, ya kaisu ga nasarar dauka a 1963.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.