BBC navigation

Da wuya Arsenal ta dauki kofi in ji Adams

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:01 GMT
tony adams

Tony Adams

Tsohon kyaftin din Arsenal Tony Adams na ganin rashin dabarar kungiyar wajen sayar da kwararrun 'yan wasanta wanda yake ganin zai yi wuya ta dauki wani kofi da hakan.

Tsohon dan wasan dan shekara 46 ya ce akwai bukatar ka rike gwanayen 'yan wasanka amma abin takaicin shi ne a shekarun nan mun bari suna ta tafiya cikin sauki.

Adams ya ce abin da ake bukata shi ne nasara, kuma ta ya ya zaka yi nasara?
Ka nada gwanayen 'yan wasa, idan ka ci gaba da sayar da su ai ba za ka dauki wani kofi ba.

Ya ce akwai 'yan wasa da yawa da Arsenal ta sayar kuma yanzu suna taka rawa sosai a kungiyoyin da suka koma.

Adams ya ce sai kungiyar ta yi da gaske ta samu ta kammala gasar Premier ta bana a cikin kungiyoyi hudu na farko sabo da babu wasu zaratan 'yan wasa a kulub din yanzu.

Kuma in har Wenger ya yi sa'a ya kai kungiyar cikin jerin kungiyoyi 4 na kan gaba a Premier to ya yi kokari sosai in ji Adams din.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.