BBC navigation

Ferrer ya lashe gasar tennis ta Paris Masters

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:38 GMT
david ferrer

David Ferrer

David Ferrer, ya lashe gasar Zakarun tennis ta Paris Masters, a karon farko inda ya doke Jerzy Janowicz.

Ferrer dan kasar Spaniya ya sami galaba ne a kan abokin karawar ta sa Janowicz dan kasar Poland a turmi biyu a jere.

Wannan shi ne kofi na bakwai da Ferrer ya dauka a wannan shekara ta 2012.

Wannan karawa ta karshe ta gasar ta Paris Masters, ta zama ta farko a tarihinta da ba wani dan wasa na Faransa.

Haka kuma wasan na karshe ya kasance na farko na Zakarun tennis na duniya, ATP Masters 1000 da babu ko daya daga cikin manyan zakarun tennis na duniya Roger Federer ko Rafael Nadal ko Novak Djokovic ko kuma Andy Murray tun shekaru biyu da suka gabata lokacin da Robin Soderlings ya yi nasara a kan Gael Monfils.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.