BBC navigation

Murray ya yi nasara a kan Tomas Berdych

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:58 GMT
Andy Murray

Andy Murray zai yi karawarsa ta farko tun bayan zama zakaran US Open

Andy Murray ya yi nasara a kan Tomas Berdych a Gasar Karshe ta ATP World Tour a London, gasarsa ta farko a gida tun bayan da ya lashe gasar US Open.

Dan wasan na tennis ne ya kawo karshen zaman jiran tsammanin da Burtaniya ta yi shekaru saba'in da shida tana yi wani namiji daga cikin 'yan wasanta na tennis ya zama zakaran Babbar Gasar Tennis, wato Grand Slam.

Murray ya yi galaba ne a kan Berdych da turmi uku bayan da abokin karawar ta sa ya yi nasara a kansa a turmin farko.

Wannan ce karawa ta farko a zagayen karshe na kakar Babbar Gasar ta bana, wadda aka fara a London.

Shi kuwa Novak Djokovic, wanda ya koma kan matsayinsa—na daya a duniya—zai kara ne da Jo-Wilfred Tsonga a wasa na biyu na rukunin farko , Group A na gasar.

Nasarar da Djokovic ya yi a kan Murray ita ta ba shi damar lashe Babbar Gasarsa ta farko a watan Satumba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.