BBC navigation

Kocin Southampton ya ce ya cancanci kora.

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:32 GMT
Nigel Adkins

Nigel Adkins

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Southampson, Nigel Adkins, ya ce ya san cewa shi ne kocin farko da za a yi waje da shi a kakar wasanni ta bana ta Gasar Premier, bayan kungiyar sa ta sha kashi sau takwas a kakar wasannin.

Kwallaye biyun da Peter Odemwingie ya ci ne a wasan da kungiyar ta buga da West Brom suka tura ta can kasan tebur.

A cewar Adkins, "Ako da yaushe akwai ya cancanci kora, idan har ka kasance a can kasan tebur, to zai iya yiwuwa kai ne".

Ya ci gaba da cewa, "Ba zan musanta haka ba, amma fa mun fuskanci babban kalubale".

Kungiyar ta Southampson ta gaza samun nasara ko sau daya tun da aka fara kakar wasanni ta bana; kuma duk da damar da suka samu a filin wasa na The Hawthorns kwallayen da Odemwingie ya ci sun karya lagonsu.

Ya zuwa yanzu a kakar wasannin ta bana, an ci kungiyar kwallaye ashirin da takwas.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.