BBC navigation

Kungiyar Chelsea ta dakatar da dan kallo

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:43 GMT
'yan kallo

'Yan Kallo

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta haramtawa wani dan kallo zuwa filin wasanta na Stamford Bridge har sai 'yan sanda sun kammala bincike a kan zargin da ake masa na laifin cin mutunci na wariyar launin fata, a lokacin wasan da kungiyar ta yi nasara a kan Manchester United na cin Kofin kalubale na Capital One, a makon da ya gabata.

Hotunan da aka dauka a lokacin wasan sun nuna dan kallon yana yin wata alama da ake dangantawa da biri da ake ganin ya yi ne domin cin mutuncin dan wasan Manchester United, Danny Welbeck.

'yan sanda sun bada belin mutumin da ake zargi da aikata laifin mai suna Gavin Kirkham, mai shekaru 28 bayan sun yi masa tambayoyi.

Sai dai Kungiyar ta Chelsea, ta ce mutumin da ake zargin ba ya daga cikin magoya bayanta da suka sayi tikitin kallon wasanninta na kakar wasan bana ko kuma shedar cewa dan kungiyar magoya bayanta ne.

A watan Mayu Klub din na Chelsea ya haramatawa wani magoyin bayansa ci gaba da zama dan kungiayar magoya bayansa na tsawon rai da rai bayan da mutumin ya amince cewa ya furta kalaman cin mutunci na wariyar launin fata ga Didier Drogba.

An jiyo mutumin mai suna Stephen Fitzwater, dan shekaru 55 yana furta kalaman lokacin karawar Chelsea da Tottenham a wasan kusa da na karshe na cin kofin Kalubale a watan Afrilu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.