BBC navigation

Matakan kawar da wariyar launin fata a wasa

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:18 GMT
mark clattenburg

Mark Clattenburg

Wata kungiya da take fafutukar kafa kungiyar 'yan wasan kwallon kafa bakaken fata ta bukaci kungiyoyin wasa da su rinka korar duk dan wasan da aka samu da laifin nuna wariyar launin fata kuma a haramtawa dan wasan wasa tsawon watanni tara.

Kungiyar lauyoyi bakaken fata ita ce ta kawo shawarar hakan a jerin matakai goma da ta tsara da ta ke ganin za a bi domin magance matsalar wariyar launin fata a fagen wasanni a Ingila.

Kungiyar kuma ta na son a rinka barin wasa a duk lokacin da wani dan kallo ya ci mutuncin dan wasa ta nuna wariyar launin fata.

Bugu da kari kungiyar ta na son a dakatar da alkalin wasa Mark Clattenburg daga alkalancin wasa har sai an kammala binciken da ake yi a kansa na nunawa 'yan wasan Chelsea wariyar launin fata.

An wallafa takardar matakan ne ya yin da ake shirin gudanar da wani taro tsakanin Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila da Kungiyar Kwararrun 'yan wasan Kwallon Kafa da Kuma 'yan kwmitin amintattu na Gasar Premier da kuma na Kungiyar Yaki da Wariyar launin fata a fagen wasanni (Kick it Out) yau.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.