BBC navigation

Lennon ya koda Celtic a kan lallasa Barcelona

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:31 GMT
neil lennon

Neil Lennon

Kocin kungiyar wasan kwallon kafa ta Celtic, Neil Lennon, ya bayyana farin cikinsa dangane da nasarar da 'yan wasansa suka samu a kan Barcelona a wasan cin Kofin Zakarun Turai.

Victor Wanyama shi ne ya fara ci wa Celtic din kwallonta ta farko san nan kuma Tony Watt wanda ya shigo daga baya ya sanya kwallo ta biyu a raga kafin daga bisani Lionel Messi ya jefawa Barcelona kwallonta daya inda wasan ya zama 2-1.

Lennon ya ce, kociyan Barcelona, Tito Vilanova, ya sanya David Villa da Cesc Fabregas ni kuma na shigo da yaro dan shekara 18 wanda muka sayo fam 50,000 kawai daga Airdrie, kuma muka rikita musu lissafi.

Yace ina ganin wannan ya zama daya daga cikin muhimman ranaku a tarihin kungiyar na yanzu.

Duk da irin hare-haren da Barcelona suka yi ta kaiwa, basu samu damar karya lagon 'yan wasan baya na Celtic ba wadanda mai tsaron gidansu ma yana kan ganiyar sa a wasan.

Kocin ya ce, 'yan wasana gwarzaye ne'',bayan an tashi daga wasan wanda yanzu ya sa maki biyu ne tsakaninsu da Barcelona da take matsayi na daya a rukuninsu na 7, wato group H, kuma suka yiwa Benfica ta uku a rukunin rata da maki uku.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.