BBC navigation

Ward ba zai bugawa Yankin Ireland wasa ba

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:50 GMT
jamie ward

Jamie Ward

Dan wasan Yankin Arewacin Ireland, Jamie Ward, ba zai buga wasan da Yankin zai yi na neman shiga gasar cin kofin Duniya da Azerbaijan, a mako mai zuwa ba.

Hukumar kwallon Kafa ta Ireland din ta tabbatar cewa dan wasan ba zai buga wasan na rukuni na 4, Group F ba sabo da ya yi rauni a cinyarsa.

Dan wasan na daga cikin wadanda aka zaba za su buga wasan da Yankin Ireland din zai yi da Azerbaijan amma kocin kungiyarsa ta Derby County, Nigel Clough, ya ce ward din ya yi rauni ba zai samu damar wasa ba.

Ya ce baya jin dan wasan zai iya murmurewa a cikin wannan makon a don haka abu ne mai wuya ya iya buga wasan na mako mai zuwa.

Hukumar Kwallon kafa ta Yankin Arewacin Irelan din ta gayya ce shi buga wasan da Azerbaijan duk da cewa baya bugawa kungiyarsa wasa tun lokacin da suka yi wasa da Nottingham a watan Satumba.

Ward,mai shekara 26, tsohon dan wasan Chesterfield da Sheffield United a watan Agusta na bara ne ya fara buga wasan kasa da kasa lokacin da yankin Ireland ya yi da Faroe Islands.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.