BBC navigation

Zimbabwe ta kafa kwamitin duba zargin Coge a wasa

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:57 GMT
zimbabwe

Zimbabwe

Hukumar Kwallon Kafa ta Zimbabwe (zifa) ta kafa kwamitin daukaka kara a kan hukunce-hukuncen laifin choge a wasannin da aka yankewa 'yan wasa da sauran jami'an wasa.

Ya zuwa yanzu 'yan wasa da jami'an wasa 15 aka yankewa hukuncin haramta musu shiga harkar wasanni har iya rayuwarsu, wasu guda 10 kuma akayi musu hukuncin haramcin na tsawon shekaru 10.

Ya yin da da galibinsu suka garzaya zuwa kotuna domin neman kotunan su bi bahasin hukuncin da kwamitin ya yanke musu kuma wasunsu suka kai kara gaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, Hukumar ta FIFA ta ce dole ne su fara gabatar da korafinsu a gaban hukumar kwallon kafa ta kasar alabashshi idan ta gama nata basu gamsu ba sai su kai gabanta.

Kwmitin na Hukumar Kwallon kafar ta Zimbabwe ya hada da lauyan da ke kare wanda ake zargi da laifi a kotun manyan laifuka ta duniya, Silas Chekera, wanda ya kare tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor a Hague.

Akwai kuma Thabani Mbofu lauya a babbar kotu da kuma kotun kolin Zimbabwe wanda kuma ya ke aiki da kotun kasa da kasa dake Rwanda.

Sai dai kuma kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Zimbabwe ta nuna damurta a kan kudin da aka sa na gabatar da bukatar daukaka kara dala 6000.

Inda sakataren kungiyar Paul Gundani ke cewa kudin ya yi yawa sosai idan aka yi la'akari da cewa akasari albashin 'yan wasan kansa dala 300 a wata, kuma wannan dala 6000 ta dara kudin shigar da kara na Hukumar FIFA ita kanta wanda ya ke dala 3000, yana mai kari da cewa 'yan wasan da ke cikin kasara ba zasu iya biyan wannan kudi ba.

A yanzu dai akwai wasu 'yan wasan da jami'an wasa 74 da da suke jiran hukuncin da za a yanke musu na laifin choge a wasanni da ya kama daga haramcin watanni 6 zuwa shekaru 5.

Wasu 'yan wasan sun amsa laifin cewa sun karbi kudade domin su bari a ci kungiyar kwallon kafa ta kasar a lokacin rangadin Asia da suka yi tsakanin 2007 da 2009.

Daga nan ne kuma aka kara fadada bincike har zuwa sauran wasannin da kungiyoyin kasar ke shiga a wajen kasar

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.