BBC navigation

Hukumar FA ta yi wa Clattenburg tambayoyi

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:39 GMT
Mark Clattenburg da John Mikel Obi

Ana zargin Mark Clattenburg da furta kalaman wariya ga John Mikel Obi

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Ingila, wato FA, ta yi wa jami'an da ke sa ido a kan wasa tambayoyi dangane da zargin da Chelsea ta yi cewa alkalin wasa Mark Clattenburg ya furta kalaman da ba su dace ba ga John Mikel Obi.

Kungiyar ta Chelsea dai ta zargi alkalin wasan ne da yin amfani da kalaman da ke nuna wariyar launin fata yayin wasan da ta sha kashi a hannun Manchester United a watan Oktoba.

A farkon mako mai zuwa ake sa ran za a yanke shawara a kan ko za a dauki mataki.

An bayar da rahoton cewa hukumar ta FA ta yi wa Clattenburg da mataimakansa da kuma wani jami'i na hudu, Michael Jones, tambayoyi.

Alkalin wasan ya musanta zargin da ake yi a kansa, an kuma ce ba daya daga cikin mataimakansa Michael McDonough da Simon Long da ya ji wani abu da ke tabbatar da zargin na kungiyar Chelsea.

Dukkan jami'ai hudu da ke sa ido a kan wasa dai kan sanya makirfon da lasifikar kunne wadanda ke ba su damar jin abin da ko wannensu ke fada yayin da ake wasa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.