BBC navigation

Kwarin-gwiwar kocinmu ce ta sa muka yi nasara, in ji Hernandez

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:11 GMT

Javier Hernandez

Dan wasan gaba na Mancheter United, Javier Hernandez, ya ce kwarin gwiwar da kocinsu ke da shi a fagen wasanni ne ya sa suka yi nasara a wasan da suka buga da Aston Villa a gasar Premier, lamarin da ya ba su damar dawowa saman tebur.

Hernandez ya zura kwallaye biyu a wasan da suka buga a filin wasa na Villa Park.

"A tarihi, Manchester United ba ta taba karaya ba,'' in ji Hernandez.

Ya kara da cewa tun da dai ana yin mintuna 90 a kowanne wasa, ba sa fitar da rai sai an kammala shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.