BBC navigation

An zargi FA da nuna wariyar launin fata

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:18 GMT

Clattenburg da Mikel

Shugaban kungiyar lauyoyi bakaken fatar Ingila, Peter Herbert, ya zargi hukumar kwallon kafar kasar (wato FA) da daurewa batun wariyar launin fata gindi, bayan da ta ki gabatarwa 'yan sanda koken da dan wasan Chelsea, John Mikel Obi, ya yi a kan alkalin wasa Mark Clattenburg na nuna masa wariyar launin fata.

Mista Herbert ya yi imanin cewa hukumar FA ba ta yi bincike kamar yadda ya kamata ba game da zargin da Obi ya yi wa Clattenburg.

Ya shaidawa BBC Radio 5 live cewa, ''Muna kallon FA a matsayin wacce ke daukaka batun wariyar launin fata".

Sai dai shugaban FA, David Bernstein, ya bayyana Herbert da cewa bai ma san abin da ke faruwa ba dangane da batun, kuma kalamansa ba su da muhimmanci.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.