BBC navigation

Ya kamata mu mayar da hankali kan kofin duniya —Eto'o

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:52 GMT

Samuel Eto'o

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Kamaru, Samuel Eto'o, ya yi kira ga kasar ta mayar da hankali kan yadda za ta cancanci shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a yi a Brazil, kana ta manta da rashin katabus din da ta yi a gasar cancantar lashe kofin Afrika.

Eto'o ya shaidawa jaridar Cameroon Tribune ranar Laraba cewa: ''Rashin nasarar da muka fuskanta a shekarun baya- bayan nan ta kashe mana jiki, amma haka da ma rayuwa take; wata rana ka sha zuma, wata rana ka sha madaci''.

Wannan shi ne karon farko da dan wasan, wanda sau hudu yana lashe kyautar zakaran kwallon kafa na Afirka, ya yi tsokaci game da gazawar da Kamaru ta yi ta cancatar shiga gasar cin kofin kasashen Afirka a watan jiya, lokacin da kasar Cape Verde ta yi nasarar cancanta.

A baya dai, Kamaru ce ke tashe a fagen kwallon kafar Afirka, amma a shekarun baya-bayan nan ta gaza yin katabus.

Eto'o ya kara da cewa: "Abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne, mu san yadda za mu gyara a nan gaba. Mu dauki darasi daga abubuwan da suka faru baya''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.