BBC navigation

'Yan sanda sun daina binciken Clattenburg

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:29 GMT

Clettenburg da Mikel

'Yan sanda birnin London sun daina binciken da suke yi wa alkalin wasa Mark Clattenburg, game da zargin kalaman wariyar launin fata da aka ce ya yi wa dan wasan Chelsea John Obi Mikel.

'Yan sandan sun ce babu wata shaida da ta nuna cewa alkalin wasan ya furta kalaman lokacin wasan da Manchester United ta doke Chelsea da ci 3 da 2.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila ta ce za ta ci gaba da binciken da ta fara yi game da batun.

Chelsea ta zargi Clattenburg da yin kalaman da ba su dace ba a kan Mikel cikinsu har da kalaman wariyar launin fata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.