BBC navigation

Song ba zai buga wasan sada zumunta ba

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:03 GMT

Alex Song

Dan wasan tsakiya na tawagar kwallon kafar Kamaru, Alex Song, ya ce ba zai buga wasan sada zumuntar da tawagar za ta yi da kasar Albania ba saboda yana fama da ciwon baya.

Dan wasan mai shekaru 25 da ke bugawa Barcelona wasa, ba zai samu damar bin takwarorinsa zuwa Geneva ba inda za a buga wasan.

A wani sakon Twitter da kungiyar Barcelona ta aike, ta ce maimakon zuwa Geneva, yanzu Song zai ci gaba da kasancewa a kulob din.

Yana cikin 'yan wasan da Barcelona ta ajiye a benci lokacin wasan da ta yi da Real Mallorca ranar Asabar lokacin da ta ci kwallaye hudu, yayin da Mallorca ta ci biyu.

Song ya fara bugawa Kamaru wasa ne a shekarar 2005, inda ya zurawa kasar kwallaye 34 a wasannin da ta buga .

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.