BBC navigation

Tagomashin Torres ya kusa karewa a Chelsea —Gullit

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:31 GMT

Fernando Torres

Tsohon dan wasan Chelsea, Ruud Gullit, ya ce tagomashin Fernando Torres ya kusa karewa a kulob din ganin cewa tun da aka saye shi kwallaye hudu kawai ya zura.

Dan wasan mai shekaru 28 ya buga dukkan wasannin Gasar Premier ta bana, inda ya yi ta kokarin zura kwallo amma sai kwallaye hudu kacal ya zura.

Hakan ne ya sanya ake ganin kocin kulob din Roberto Di Matteo zai maye gurbinsa da dan wasan Atletico Madrid, Radamel Falcao, wanda ake sa ran sayen sa nan ba da dadewa ba.

Gullit ya ce, " Abin mamaki ne ganin yadda dan wasan gaban ya kasa zura wa Chelsea kwallaye akai-akai, bayan mun sani cewa ya yi fice lokacin da yake bugawa Atletico da Liverpool wasa, kafin Chelsea ta saye shi a kan fam miliyan 50 a shekarar 2011''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.