BBC navigation

Manchester City za ta kare kambunta - Vieira

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:42 GMT

Patrick Vieira

Jami'in da ke kula da ci gaban kwallon kafa na kulob din Manchester City, Patrick Vieira, ya ce daidai kulob din yake da ya kare kambunsa a gasar Premier ta Ingila.

Akwai tazarar maki biyu tsakanin City da Manchester United, wanda shi ne ke gaba kakar wasa ta bana.

Amma duk da haka Vieira ya ce kocin kulob din, Roberto Mancini, yana yin iya bakin kokarinsa don ganin kulob din ya kare matsayinsa.

Ya kara da cewa a shirye Mancini yake ya jajirce don ganin kulob din ya cigaba da samun daukaka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.