BBC navigation

Djokovic ya sadaukar da nasararsa ga mahaifinsa

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:28 GMT
Novak Djokovic

Novak Djokovic ya bayyana yadda mahaifinsa ya karfafe shi

Dan wasan tennis na daya a duniya Novak Djokovic ya sadaukar da nasararsa a kan Roger Federer a Gasar ATP World Tour ga mahaifinsa wanda ba shi da lafiya.

Dan wasan na kasar Serbia ya lallasa Federer da ci 7-6 (8-6) 7-5 ne; hakan ne kuma ya ba shi damar yin nasara a gasar ta karsen kaka a filin O2 Arena na birnin London.

Daga bisani dan wasan ya bayyana yadda mahaifinsa Srdjan, wanda ya ce yana fama da matsananciyar cutar da ta shafi kafar numfashinsa, ya karfafa shi.

"Wannan nasarar tasa ce", inji dan wasan mai shekaru ashirin da biyar daga Belgrade.

Ya kara da cewa, "Yanzu ya samu sauki—akwai lokacin da jikinsa ya yi tsanani sosai. Ba mu san abin da gobe za ta yi ba, amma dai yanzu yana samun sauki".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.