BBC navigation

Za mu yi wa Arsenal garambawul —Gazidis

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:23 GMT

Ivan Gazidis

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafar Arsenal, Ivan Gazidis, ya tabbatarwa magoya bayan kungiyar cewa zai yi mata garambawul yadda za ta iya fafatawa da kowacce kungiya a kakar wasannin da ke tafe.

Kulob din ya gaza lashe Gasar Premier tun shekarar 2005, kuma ya fara kakar wasanni ta bana da kafar hagu.

Gazidis ya shaidawa BBC cewa: ''Muna shiryawa sosai don tunkarar duk wata kungiya nan da shekaru biyu zuwa uku''.

Ya kara da cewa kungiyar Arsenal za ta shiga harkokin kasuwanci domin kara samun kudin da za ta yi amfani da su wajen inganta wasanta a kakar wasannin da ke tafe.

A da dai ana zargin shugabannin kungiyar da mayar da hankali wajen cin riba, ba lashe wasanni ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.