BBC navigation

Suarez ba zai bar Liverpool ba —Rodgers

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:45 GMT

Luiz Suarez

Manajan Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce Luis Suarez zai ci gaba da kasancewa a kulob din, yana mai cewa ba za a sanya shi a kasuwar 'yan wasa a watan Janairu ba.

An yi ta tsokaci cewa Suarez, mai shekaru 25, yana da aniyar komawa Manchester City.

Sai dai Rodgers ya ce: "Babu wanda zai taya shi bare ma a saye shi. Luis Suarez zai ci gaba da zama a nan."

Suarez ya samu tagomashi sosai a kulob din a kakar wasa ta bana, har ma ya zura kwallaye 11 a wasanni 16 da ya buga.

Yana daya da cikin 'yan wasa biyu da suka fi cin kwallaye - ya zura kwallaye takwas a gasar Premier ta bana.

Rodgers ya kara da cewa: "Idan muka bar Luis ya tafi, ba mu da dan wasan gaba; don haka ba zan bar shi ya bar kulob din ba. Tabbas, ba ya cikin 'yan wasan da nake son sayarwa''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.