BBC navigation

An raunata 'yan wasan Zambia a Afirka ta Kudu

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:48 GMT

Kennedy Mweene

An raunata 'yan wasan kwallon kafar Zambia ranar Laraba da daddare a wani hari da aka kai wa motar da suke ciki bayan kammala wasan sada zumuntar da suka yi da Afirka ta Kudu, wanda suka lashe da ci daya.

Mai tsaron gidan tawagar, Kennedy Mweene, ya samu rauni a kansa, lokacin da wadansu mutane da ba a san su ba suka yi jifa cikin motar har suka fasa gilashinta.

Shi ma dan wasan gaba, Felix Katongo, ya samu rauni.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu, SAFA ta ce an kama yara biyu - daya mai shekaru 12, daya mai shekaru 13 sanadiyar aukuwar wannan lamari.

Shugaban SAFA, Kirsten Nematandani, ya nemi afuwar Zambia sanadiyar wannan hari da aka kai.

Ya ce:''Wannan abin kunya da ya faru bakon abu ne a hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu, kuma ya yi illa ga martabar tawagar mu da ma kasar baki daya''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.