BBC navigation

Al Ahly ta lashe kofin zakarun Afirka

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:24 GMT

'Yan wasan al Ahly

Tawagar kwallon kafar Masar, Al Ahly, ta bai wa takwararta ta Tunisia Esperance mamaki yayin da ta doke ta da ci 2 da 1 a gasar lashe kofin zakarun Afirka.

Esperance ce ke rike da kofin wanda ta lashe sau biyu a jere.

Dan wasan Al Ahly, Gedo, ne ya zura kwallon farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Walid Soliman ya zura kwallo ta biyu.

Wannan shi ne karo na bakwai da Al Ahly ke daukar kofin gasar zakarun Afirka

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.