BBC navigation

Manchester City na taka rawar-gani —Mancini

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:48 GMT

Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce kungiyar tana taka rawar-gani bayan da ta doke Aston Villa da ci biyar babu ko daya a wasan gasar Premier da suka buga ranar Asabar.

A makon jiya City ta doke Tottenham, lamarin da ya sanya Mancini ya ce 'yan wasan kungiyar na tagazawa a kan kokarin su na baya.

Mancini ya ce: "Za mu taka rawa fiye da yadda muka fara kakar wasa ta bana. Ina fata za mu kwata abin da muka yi a kakar wasa ta badi. An samu sauyi a wasanni biyu da muka yi. Mun samu kwarin gwiwa kamar shekarar da ta gabata."

Nasarar da Manchester City ta yi ta ba ta damar darewa saman tebur, yayin da makwabciyarta, Manchester United, ta rikito daga tebur din sakamakon cin da Norwich ta yi mata na kwallo daya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.