BBC navigation

McClean: 'Yan sanda sun fara bincike kan zargin kisa

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:47 GMT

James McClean

'Yan sandan yankin Northumbria sun fara bincike bayan dan wasa, James McClean, ya yi zargin cewa wani ya yi barazanar kashe shi.

Dan wasan gaban na Sunderland ya yi ikirarin cewa wani mutum ne ya aike masa sakon Twitter yana barazanar kashe shi bayan da ya ki sanya wani bajo - na tunawa da 'yan mazan jiya- lokacin wasan da kulob din ya ci Everton biyu da daya ranar 10 ga watan Nuwamba.

Wadansu magoya bayansa sun yi wa da wasan mai shekaru 23 ihu lokacin da aka sanya shi a wasan da suka buga ranar Lahadi wanda Sunderland ta ci Fulham uku da daya .

Kakakin 'yan sandan ya shaidawa Sky Sports cewa: "'Yan sanda na yi wa wadansu mutane tambayoyi bayan da aka samu rahoton zargin yunkurin kisan kai da aka yi wa dan wasan ta kafar sada zumunta. Jami'anmu sun yi wa wadansu shugabannin Sunderland tambayoyi, kuma muna ci gaba da gudanar da bincike."

Kocin Sunderland, Martin O'Neill, ya yi tsokaci game da batun, yana mai goyon bayan dan wasansa.

Ya shaidawa manema labarai cewa: "James zai yi nasara a kan wannan batu. Hakan ya faru ne saboda abin da ya faru a makon jiya - watau matakin da ya dauka na kin sanya bajo. Ya kamata a sani cewa kowa na da zabi na abin da zai yi ko yaki yi.''

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.