BBC navigation

David Beckham zai bar LA Galaxy a watan gobe

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 10:16 GMT
David Beckham

David Beckham ya ce zai bar LA Galaxy a watan gobe

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham zai bar kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Galaxy a watan gobe bayan ya kwashe shekaru shida yana buga musu wasa.

Dan wasan mai shekaru talatin da bakwai da haihuwa, ya daura aniyar barin kungiyar ce bayan wasan karshe na cin Kofin Gasar Major League Soccer (MLS) ta Amurka ranar 1 ga watan Disamba.

A wata sanarwa da ya fitar, Beckham ya ce: "Ina so in fuskanci kalubale daya kafin in janye daga sana'ar buga kwallo".

Kungiyar kwallon kafa ta Melbourne Heart ta yi ikirarin cewa tana tattaunawa da Beckham don ya buga mata wasanni goma a Australia, duk da cewa dan wasan ya ce ba shi da niyyar buga wasa a Gasar A League.

Shugaban kungiyar ta Heart, Scott Munn, ya shaidawa BBC cewa: "Da gaske muke yi kuma muna aiki ba ji ba gani tare da wakilan David don gabatar masa da wani tayi da ya dace da kimarsa ta dan wasan da ya shahara a duniya.

"Muna tattaunawa da David dangane da wasanni goma".

Kungiyarsa ta farko

Yana dan shekaru goma sha hudu Beckham ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, wacce ya bugawa wasanni dari uku da casa'in da takwas; yana bugawa kungiyar kuma lokacin da ta lashe Gasar Premier har sau shida da kuma Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

A shekara ta 2003 ya koma Real Madrid a bisa wani kwantiragin fam miliyan ashirin da biyar, ya kuma taimakawa kungiyar lashe Gasar La Liga a shekarar 2007, makwanni kadan kafin ya koma Amurka.

Ya fara bugawa Ingila wasa ne a shekarar 1996 a wasan da ta yi da Moldova, ya kuma zama kyaftin din tawagar daga shekarar 2000 zuwa 2006.

A shekarar 2009 ya buga wasansa na dari da goma sha biyar kuma na karshe a tawagar ta Ingila, wasan da Ingila ta lashe da ci uku da nema.

Beckham ya kara da cewa: "Ba na daukar wannan mataki a matsayin karshen alaka ta da gasar MLS saboda buri na shi ne a dama da ni nan gaba a matakin mallakar kungiyoyi".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.