BBC navigation

Chelsea ta kori Roberto Di Matteo

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:18 GMT
Di Matteo

Di Matteo ya lashe gasar zakarun Turai da FA a matsayinsa na kocin riko bara

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta raba-gari da kocinta Roberto Di Matteo, bayan da suka sha kashi da ci 3-0 a hannun Juventus a gasar zakarun Turai, kamar yadda sanarwar kulob din ta ce.

Di Matteo ya lashe gasar zakarun Turai da kuma FA a matsayinsa na kocin riko bara, sannan aka bashi kwantiragin shekaru biyu a watan Juni.

Sai dai biyo bayan kashin da suka sha a hannun Juventus da ci 3-0, wanda ya jefa kulob din cikin hadarin ficewa daga gasar a rukunin farko, a yanzu ya rasa aikinsa a Stamford Bridge.

Phil McNulty

Koda a yadda a Roman Abramovic yake gudanar da ayyukansa, korar Roberto Di Matteo bata dace ba.

Shi ne mutumin da ya lashe gasar zakarun Turai da FA a watan Mayu.

Sanarwar Chelsea ta nuna cewa kulob din baya taka rawar gani kamar yadda ya kamata.

Amma wata guda da ya wuce, sune ke jagorantar teburin Premier bayan da suka doke Spurs da ci 4-2.

"Kulob din zai fitar da sanarwa nan gaba kadan kan wanda zai maye gurbinsa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Mai kulob din Roman Abramovich, wanda ke neman koci na tara tun bayan da ya sayi kungiyar a shekara ta 2003, ya tuntubi tsohon kocin Liverpool Rafael Benítez, kan ko zai jagoranci kulob din na gajeran lokaci.

Rahotanni sun ce Abramovich, wanda dan kasar Rasha ne ya tattauna da Benitez ne kafin kashin da Chelsea ta sha a ranar Talata a Italy, a kokarin da yake na duba makomar kulob din.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.