Zaɓen gwarzon ƙwallon Afrika na BBC na 2012

Zaben gwarzon kwallon Afrika na BBC na 2012

An bayyana sunayen 'yan wasa biyar din da ke takarar zamowa gwarzon dan kwallon Afrika na BBC a shekara ta 2012.

Yaya Toure ya samu shiga ciki a karo na biyu a jere, inda zai fafata da takwaransa na Ivory Coast Didier Drogba, dan wasan Senegal Demba Ba, da Younes Belhanda na Morocco da kuma kyaftin din Zambia Christopher Katongo.

Masu sha'awar kwallon kafa a Afrika na da damar kada kuri'unsu ga wanda suke so daga ranar 22 ga watan Nuwamba zuwa ranar Alhamis 13 ga watan Disamba na 2012 ta hanyar latsa wannan shafin

Christopher Katongo

Christopher Katongo

Shekaru goma da suka wuce sun zamo mafiya muhimmanci ga kyaftin din tawagar Zambia, da ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika ta 2012 Christopher Katongo.

Katongo ya fara yin fice ne a kulob din Green Buffaloes na Zambia a shekara ta 2003 da 2004.

A daya daga cikin rawar da ya taka, ya zura kwallaye hudu a gasar Confederation Cup 2003/2004 lokacin da suka doke Saint Michel na Seychelles da DC Motema Pembe na DR Congo 5-0 da kuma 6-1.

Sabanin sauran takwarorinsa na Zambia da suka taso a tawagar matasan kasar, Katongo ya fara ne daga tawagar 'yan kasa da shekaru 23.

Ya fara taka leda a gasar cin kofin Afrika a Masar a shekara ta 2006 inda aka fitar da Zambia a rukunin farko, amma duk da haka ya zura kwallo daya a wasan da suka doke Afrika ta Kudu.

Shekara daya bayan haka ya zira kwallaye uku inda suka doke Afrika ta Kudu da ci 3-1 a Cape Town a wasan share fagen shiga gasar Afrika ta 2008.

A matakin Kulob kuwa, ya taka leda a Jomo Cosmos na Afrika ta Kudu daga 2004 zuwa 2007.

A Turai kuwa, ya buga kwallo a kulob din Brondby na Denmark a 2007 kafin ya koma Arminia Bielefeld na Jamus a 2008.

A shekara ta 2010, ya bar Jamus zuwa Girka inda ya shafe shekara guda a Skoda Xanthi kafin daga bisani ya koma China a 2011 inda a yanzu yake taka leda a kulob din Henan Construction.

Domin samun karin bayani latsa nan

Demba Ba

Demba Ba

Demba Ba ya nuna kwarin gwiwa da juriya da kwarewa wurin zura kwallaye, abin da ya ba shi damar kasancewa daya daga cikin 'yan wasan da ke haskakawa a Newcastle.

Kuma wannan ne ya sa ya ja hankalin mutane da dama har ya kai ga samun gurbi a jerin 'yan wasan da za a kada kuri'a a kansu.

Dan wasan na kasar Senegal mai shekaru 27 ya taka rawar gani matuka tun lokacin da ya koma Newcastle daga West Ham a shekara ta 2011.

Ya zura kwallaye 16 a shekara ta farko inda ya kasance dan wasan da ya fi kowanne zura kwallaye a kulob din—abin da ya taimaka wa Newcastle ta kare kakar a mataki na biyar, sannan ta samu damar shiga Gasar Cin Kofin Europa.

Duk da cewa ba kowanne wasa aka fara da shi ba a kakar bana, Ba ya zura kwallaye takwas a wasanni 12 da ya buga—inda ya zamo wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din kuma na biyu a gasar baki daya.

Ba, wanda aka haifa a Faransa, ya fara taka wa Senegal leda ne a wasanta da Tanzania a watan Yunin 2007, kuma ya zura kwallaye hudu a wasanni 16 da ya buga.

Yana cikin 'yan wasan gaba da kasar take da su, inda yake neman gindin zama tare da abokin wasansa na Newcastle Papiss Cisse da kuma Moussa Sow da Dame N'Doye da Moussa Konate.

Sai dai Ba da abokan wasansa ba za su halarci Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka da za a yi a Afirka ta Kudu ba, bayan da aka ladabtar da kasar sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan wasan share fagen da suka buga da Ivory Coast.

A maimakon haka, Demba Ba zai yi kokarin ganin cewa ya taimaka wa Newcastle ta dago sama a teburin Gasar Premier ta bana.

Domin samun karin bayani latsa nan

Didier Drogba

Didier Drogba

A watan Mayun bana, Didier Drogba ya bar Chelsea bayan ya shafe shekaru takwas tare da kasancewa dan wasan da ya fi kowa taka rawar gani a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Didier Drogba, wanda aka baiwa jan kati shekaru hudu da suka wuce a makamancin wannan wasa, ya zura fanaretin karshe da ya baiwa Chelsea damar lashe Gasar Zakarun Turai a karon farko a tarihinta.

Dan wasan mai shekaru 34 ya bar Ingila bayan ya kafa tarihi zuwa kulob din Shanghai Shenhua na kasar China.

Rahotanni sun ce yana karbar fam 200,000 a kowanne mako, inda ya zura kwallaye takwas a wasanni 11.

Rawar da Drogba ya taka a birnin Munich ta sha bamban da bakin cikin da ya fuskanta watanni kadan kafin nan, lokacin da yake taka leda a kasarsa a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka.

Ya jagoranci tawagar zuwa wasan karshe a karo na biyu. Kamar a kasar Masar shekaru shida da suka wuce, bugun fanareti ne ya raba tsakani.

A wannan karon Zambia ce ta sha gaban Drogba.

A tsawon lokacin da ya shafe a Chelsea, Drogba ya zura kwallaye fiye da 150 a kusan wasanni 350. Ya lashe Gasar Premier sau uku, FA sau hudu da kuma League Cup sau biyu.

A watan Oktoba magoya bayan Chelsea suka zabe shi dan wasan da ya fi kowanne taka rawa a tarihin kulob din.

Drogba ya taba lashe kyautar Zakaran Kwallon Afirka na BBC a shekara ta 2009.

Domin samun karin bayani latsa nan

Yaya Toure

Yaya Toure

Bayan da ya tallafa wa Manchester City ta lashe kofi a karo na farko a cikin shekaru 35, lokacin da ya zura kwallo daya tilo a wasan da suka lashe kofin FA a Wembley, Yaya Toure ya kuma taka rawar gani wurin taimakawa Man City lashe Gasar Premier a karo na farko.

Dan wasan tsakiyar na Ivory Coast na sahun gaba wurin kawo karshen shekaru 44 da City ta shafe ba tare da lashe gasar League ba.

Toure ya taka rawar gani a wasan da Man City ta doke abokiyar hamayyarta Manchester United, sannan ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Newcastle da ci biyu ba ko daya.

Wannan ne kofi na baya-bayan nan da dan wasan mai shekaru 29 ya dauka, bayan da ya lashe Gasar Zakarun Turai, Super Cup, kofin kulob din zakarun duniya, Gasar La Liga ta Spain da Copa del Rey da ya lashe a Barcelona da kuma gasar League ta Girka da ya lashe da Olympiakos.

Toure, wanda ya lashe kyautar zakaran dan kwallon Afirka na Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta CAF a 2011, ya fara kakar bana da kafar dama.

Ya zura kwallo a wasan da City ta doke Chelsea a gasar cin kofin Community Shield, sannan ya zura karin kwallaye hudu a gasar Premier.

A watan Janairu, zai yi kokarin ganin ya lashe Gasar Cin Kofin Afirka da tawagar Ivory Coast.

Domin samun karin bayani latsa nan

Younes Belhanda

Younes Belhanda

Idan gwarzon duniya Zinedine Zidane ya yaba maka, babu shakka kana yin abin da ya dace—kuma babu shakka Younes Belhanda ba zai manta da kakar bana ba.

Dan wasan mai shekaru 22 na cikin muhimman 'yan wasan da suka taka rawar gani a nasarar da Montpellier ta yi ta lashe gasar Ligue 1 a karon farko cikin kusan shekaru 100 tun kafa kungiyar.

Da yake taka leda a matsayin takwaran Olivier Giroud, dan wasan na Morocco ya zura kwallaye 12 a wasanni 26—bakwai daga ciki gab da za a kammala gasar bayan dawowarsa daga Gasar Cin Kofin Afirka.

Ganin yadda yake da baiwa da kwarewa a fagen kwallo, Belhanda daya ne daga cikin shahararrun 'yan wasan Morocco a Gasar Cin Kofin Afirka ta 2012—inda ya zura kwallo a wasansu da Nijar.

Sai dai rawar da ya taka a Montpellier ce ta haskaka shi inda ya shiga sahun 'yan wasa goma sha daya da suka fi kowa taka leda a gasar Ligue 1.

Ya kuma zamo dan wasa matashi da ya fi kowanne taka leda a gasar a bara.

Daga cikin wadanda suka taba lashe wannan kyautar a baya, sun hada da Eden Hazard da Franck Ribery da Thierry Henry da kuma Zidane da kansa, a don haka Belhanda na alfahari da ita.

Montpellier ba ta yin kokari sosai bana, amma tsohon dan wasan na tawagar matasa ta Faransa na ci gaba da haskakawa.

Ya zura kwallaye hudu a wasanni 10 a gasar League—da kuma kwallaye biyu a wasanni hudu na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, wacce yake halarta a karon farko.

Domin samun karin bayani latsa nan

Za a bayyana dan wasan da ya yi nasara a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba.

Duka 'yan wasan sun taka rawar gani a kakar bana, inda hudu daga cikin biyar suka lashe lambobin yabo.

Drogba ya ci fanaretin karshe da ya baiwa Chelsea damar lashe gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko a tarihin kulob din, sannan ya zura kwallon da ta taimaka musu suka lashe gasar kofin FA.

Takwaransa na Ivory Coast Yaya Toure, ya tallafawa Manchester City wurin lashe gasar Premier League a karon farko cikin shekaru 44.

Shi ma Belhanda ya lashe gasar Ligue 1 ta Faransa inda ya zira kwallaye 12 da suka taimakawa Montpellier samun nasara a karon farko cikin kusan shekaru 100 da kafa kulob din.

A matakin kasa-da-kasa kuwa, Katongo ya jagoranci Zambia ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika, inda suka doke Ivory Coast a bugun fanareti.

Demba Ba bai taka rawar gani a gasar cin kofin Afrika ba, inda aka fitar da Senegal a zagayen farko, sai dai ya taka rawar gani a Newcastle, inda suka kare kakar wasannin bara a mataki na biyar tare da zira kwallaye 17.