BBC navigation

Takaitaccen tarihin Didier Drogba

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:52 GMT
Didier Drogba

Didier Drogba ya taka rawar gani a kakar bana

A watan Mayun bana, Didier Drogba ya bar Chelsea bayan shafe shekaru takwas tare da kasancewa dan wasan da ya fi kowa taka rawar gani a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Didier Drogba, wanda aka baiwa jan kati shekaru hudu da suka wuce a makamancin wannan wasa, ya zira fanaretin karshe da ya baiwa Chelsea damar lashe gasar zakarun Turai a karon farko a tarihinta.

Dan wasan mai shekaru 34, ya bar Ingila bayan ya kafa tarihi zuwa kulob din Shanghai Shenhua na kasar China.

Rahotanni sun ce yana karbar fan 200,000 a kowanne mako, inda ya zira kwallaye takwas a wasanni 11.

Rawar da Drogba ya taka a birnin Munich ta sha bambam da bakin cikin da ya fuskanta watanni kadan kafin nan, lokacin da yake taka leda a kasarsa a gasar cin kofin kasashen Afrika.

Ya jagoranci tawagar zuwa wasan karshe a karo na biyu. Kamar a kasar Masar shekaru shida da suka wuce, bugun fanareti ne ya raba tsakani.

A wannan karon Zambia ce ta sha gaban Drogba.

A lokacin da ya shafe a Chelsea, Drogba ya zira kwallaye fiye da 150 a kusan wasanni 350. Ya lashe gasar Premier sau uku, FA sau hudu da kuma League Cup sau biyu.

A watan Oktoba, magoya bayan Chelsea sun zabe shi dan wasan da ya fi kowanne taka rawa a tarihin kulob din.

Drogba ya taba lashe kyautar zakaran kwallon Afrika na BBC a shekara ta 2009.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.