BBC navigation

Takaitaccen tarihin Christopher Katongo

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:35 GMT
Katongo

Christopher Katongo ya taka rawar gani a nasarar da Zambia ta samu

Shekaru goma da suka wuce sun zamo mafiya muhimmanci ga kyaftin din tawagar Zambia, da ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika ta 2012 Christopher .

Katongo ya fara yin fice ne a kulob din Green Buffaloes na Zambia a shekara ta 2003 da 2004.

A daya daga cikin rawar da ya taka, ya zira kwallaye hudu a gasar Confederation Cup 2003/2004 lokacin da suka doke Saint Michel na Seychelles da DC Motema Pembe na DR Congo 5-0 da kuma 6-1.

Sabanin sauran takwarorinsa na Zambia da sukan taso ta tawagar matasan kasar, Katongo ya fara ne daga tawagar 'yan kasa da shekaru 23.

Ya fara taka leda a gasar cin kofin Afrika a Masar a shekara ta 2006 inda aka fitar da Zambia a rukunin farko, amma duk da haka ya zira kwallo daya a wasan da suka doke Afrika ta Kudu.

Shekara daya bayan haka ya zira kwallaye uku inda suka lashe Afrika ta Kudu ta ci 3-1 a Cape Town a wasan share fagen shiga gasar Afrika ta 2008.

A matakin Kulob kuwa, ya taka leda a Jomo Cosmos na Afrika ta Kudu daga 2004 zuwa 2007.

A Turai kuwa, ya buga kwallo a kulob din Brondby na Denmark a 2007 kafin ya koma Arminia Bielefeld na Jamus a 2008.

A shekara ta 2010, ya bar Jamus zuwa Girka inda ya shafe shekara guda a Skoda Xanthi kafin daa bisani ya koma China a 2011 inda a yanzu yake taka leda a kulob din Henan Construction.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.