BBC navigation

'Yan wasan Rwanda sun ci abinci mai guba

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:55 GMT

Wasan cin kofin kalubalen kudancin kasashen Afirka

Wadansu 'yan wasan tawagar kwallon kafar Rwanda sun ci abinci mai guba, gabanin wasan da za su buga a Gasar cin kofin kalubalen kasashen kudancin Afirka.

Kocin tawagar kwallon kasar, Milutin Sredojovic, ya yi matukar damuwa, bayan 'yan wasan guda hudu sun ci abinci mai guba kwanaki kadan kafin tafiyarsu Uganda inda za a yi wasan.

'Yan wasan sun hada da Emery Bayisenge, da Djabir Mutarambirwa, da Michel Rusheshangoga da kuma Barnabe Mubumbyi.

Sun ci abinci mai guba ne a otal din tawagar da ke Kigali.

An shaidawa hukumar kula da kwallon kafa da ma'aikatar harkokin wasannin kasar faruwar lamarin, kuma sun sauyawa dukkan 'yan wasan tawagar wurin zama.

Kocin tawagar ya ce rashin 'yan wasan guda hudu a gasar zai yi gagarumin tasiri a kan ta, musamman ganin cewa za ta fafata da tawagogin kasashen Uganda, da Malawi da kuma Sudan - wadanda ba kanwar-lasa ba ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.