BBC navigation

Clattenburg bai aikata laifi ba —FA

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:38 GMT

Clattenburg da Obi

Hukumar kwallon kafar Ingila, FA, ta wanke alkalin wasa Mark Clattenburg daga zargin da John Mikel Obi ya yi cewa ya furta masa kalaman wariyar launi fata.

Kungiyar Chelsea ta zargi Clattenburg da gayawa Obi kalaman ne a lokacin wasan da Manchester United ta ci kungiyar 3 da 2.

A maimakon ta hukunta Clattenburg, hukumar ta FA ta tuhumi Mikel, mai shekaru 25 a duniya, da aikata munanan dabi'u bayan wasan.

FA ta gana da Clattenburg, da Mikel, da kuma wadansu 'yan wasan Chelsea game da batun kafin ta yanke hukunci.

Clattenburg, mai shekaru 37 a duniya, ya musanta zargin da Obi ya yi, kuma rundunar 'yan sandan birnin London ta daina binciken da ta fara yi a kan lamarin a farkon watan da muke ciki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.