BBC navigation

Chelsea na neman aron Drogba

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:10 GMT

Didier Drogba

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta fara tattaunawa don yiwuwar aron tsohon dan wasan gabanta, Didier Drogba, wanda ke bugawa tawagar kasar Sin, Shanghai Shenhua wasa.

Drogba, mai shekaru 34, yana so ne ya samu kungiyar da za ta karbi aron sa gabanin Gasar cin kofin kasashen Afirka da za a yi a shekarar 2013, ganin cewa tawagar Shenhua ta kammala kakar wasanta ta bana.

Dan wasan kasar Ivory Coast din ya nemi izinin Fifa don ya samu kungiyar da za ta karbi aron sa kasancewa wa'adin da ta sanya na aron 'yan wasa ya kare.

Chelsea dai tana fama da karancin 'yan wasan gaba saboda Fernando Torres ba shi da kuzari, kana Daniel Sturridge ya samu rauni.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.