BBC navigation

FIFA ta yi watsi da bukatar Drogba

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:56 GMT

Didier Drogba

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ki amincewa da bukatar da Didier Drogba ya yi ta barinsa ya koma wata kungiya a matsayin aro gabanin gasar cin kofin kasashen Afirka a shekarar 2013.

Drogba ya mika bukatar ne duk da cewa ba a bude kasuwar aron 'yan wasa ba.

Ya ce yana so ya koma wata kungiyar ce domin ya samu damar motsa jikinsa, ganin cewa an kammala kakar wasanni a tawagar da yake yi wa wasa, watau Shenghai Shenhua ta kasar Sin.

A wata sanarwa da FIFA ta fitar, ta ce dokarta ta bai wa 'yan wasa damar zuwa aro wata kungiyar ce kawai sau biyu a shekara, kuma lokacin aron 'yan wasan ya wuce.

Ranar Alhamis, gabanin sanarwar da FIFA ta fitar, tsohuwar kungiyar da Drogba ke bugawa wasa, Chelsea, ta ce tana tattaunawa a kan yiwuwar aron sa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.