BBC navigation

Ba na tantamar aiki na — Mancini

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:40 GMT

Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce ba ya shayin yiwuwar korarsa daga kungiyar duk da cewa an fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai.

City da Real Madrid sun tashi da ci daya da daya a wasan da suka yi, lamarin da ya sanya Real da Borussia Dortmund suka haye zuwa mataki na gaba a rukuninsu, yayin da Manchester City ta fita daga gasar.

Da aka tambayi Mancini game da yiwuwar sallamarsa daga aiki sakamakon gazawar kungiyar sai ya ce: "Bana jin tsoron hakan. Idan ana yin tunanin cewa za mu lashe gasar zakarun Turai shekaru biyu kacal da fara ta, lallai mu mahaukata ne."

Shi kuwa kocin Real Madrid, Mourinho, mamaki ya yi na fitar da Manchester City daga gasar duk da makudan kudi da suka kashe wajen shirya mata .

Ya ce: "Abin mamaki da City suka gaza kai wa mataki na biyu cikin shekaru biyu a jere duk da kwararrun 'yan wasan da suke da su.

''Na yi amanna Roberto zai ci gaba da aiki ba tare da wata matsala ba. Da Real ce ta fita da 'yan jarida sun yi ta yama-didi - ba za su bar ni na dawo Madrid ba,'' in ji Morinho, wanda ke dariya lokacin da ya yi wannan kalami.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.