BBC navigation

An yiwa Benitez ihu da ele

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:44 GMT
Rafael Benitez

Rafael Benitez ya sha ihu a Stamford Bridge

Ga alama sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Rafael Benitez, ya fara saka da mugun zare, don kuwa ana gaf da fara wasan kungiyar da Manchester City ranar Lahadi aka yi masa ihu da ele a Stamford Bridge.

An tashi wasan ne dai canjaras ba ci, kuma sabon kocin na Chelsea ya amince da abin da kocin City, Roberto Mancini, ya fada cewa cin dukkanin wasannin da zai buga ne kawai zai sa Benitez ya yi farin jini a wajen magoya bayan Chelsea.

A wannan makon ne dai tsohon kocin na Liverpool ya maye gurbin Roberto Di Matteo wanda aka sallama bayan kungiyar ta ci wasanni biyu kacal a cikin takwas din da ta buga.

Sai dai kuma magoya bayan kungiyar ta Chelsea da dama ba su yi na'am da zuwan sabon kocin ba.

Dangantakar Benitez da Chelsea ta yi tsami ne lokacin da aka kara tsakaninta da kungiyarsa ta Liverpool a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, al'amarin da ga alama magoya bayan kungiyar ta London ba su manta ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.