BBC navigation

Cecafa: Burundi ta casa Somalia

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 21:09 GMT

Burundi ta fara wasanninta a gasar cin babban kofin kalubale na hukumar kwallon kafa ta gabashi da tsakiyar Afirka da kafar dama, bayan da ta lallasa Somalia da ci biyar da daya a Kampala, babban birnin kasar Uganda.

Tawagar 'yan wasan Somalia, wacce ke karkashin jagorancin tsohon mataimakin kocin Uganda, Sam Ssimbwa, ta yi ta tuntube ne a wasan nata da tawagar Burundin da ta lallasa ta da ci hudu da daya a Dar es Salam bara.

Kafin tafiya hutun rabin lokaci ne dai 'yan wasan Burundi suka zura kwallaye biyu a ragar 'yan Somalia.

Yan wasan na Somalia sun farke ci guda jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ta hanayr bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.