BBC navigation

Beckham: Harry bai fid da rai ba

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:02 GMT
David Beckham

David Beckham

Harry Redknapp ya ce ya yi amanna David Beckham zai iya buga wasa a Gasar Premier, kuma bai fitar da tsammani ba da yiwuwar samun tsohon kyaftin din na Ingila ya sa hannu a kan wani kwantiragi na bugawa Queens Park Rangers.

A watan Disamba ne dai Beckham zai bar kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Galaxy, an kuma alakanta shi da wani yunkuri na komawa kungiyar ta QPR tun bayan da Redknapp ya fara jagorantarta.

Redknapp ya shaidawa tashar kai-tsaye ta BBC 5 cewa: "Na tabbatar zai iya bugawa a Gasar Premier.

A watan Janairun 2011 Redknapp ya yi yunkurin aro Beckham lokacin yana kocin Tettenham, amma dan wasan mai shekaru atisaye kawai ya yi da kungiyar ta arewacin birnin London.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.