BBC navigation

Vettel ya lashe F1 karo na uku a jere

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:32 GMT
Sebastian Vettel

Sebastian Vettel: "Ko an tsikare ni ba zan ji komai ba"

Dan tawagar Red Bull, Sebastian Vettel, ya lashe Gasar Tesren Motoci ta Formula 1 a karo na uku a jere.

Nasarar da ya yi ta shan gaban direbobin duniya ta biyo bayan yunkurowar da ya yi ne a gasar Grand Prix ta Brazil, bayan da aka baro shi a baya a zagayen farko.

Abokin hamayyarsa Fernando Alonso na Ferrari ne ya zo na biyu.

Da wannan sakamako dai Vettel ya zamo direba mafi karancin shekaru a tarihi da ya lashe gasar sau uku a jare; shi ne kuma direba na uku da ya lashe gasar sau uku a jere a tarihi.

Vettel ya bayyana cewa: "Abu ne mai wuya a iya kwatanta abin da ke cikin zuciyata; kai, yadda nake ji yanzu haka, ko an tsikare ni ba zan ji komai ba".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.