BBC navigation

An kai Issa Hayatou kotu

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:19 GMT
Issa Hayatou da Jacob Zuma

Shugaban CAF Issa Hayatou da Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu

An kalubalanci wata doka mai cike da ka-ce-na-ce wadda ta baiwa shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) mai ci damar ci gaba da zama a kan mukaminsa a gaban Kotun Shiga Tsakani ta Wasanni (CAS).

An bukaci kotun ne ta yi nazari a kan gyaran fuskar da aka yiwa dokar cancantar tsayawa takarar shugancin hukumar ta CAF—gyaran da ya haramtawa akasarin masu tsayawa damar kalubalantar Issa Hayatou.

Tun shekarar 1988 Hayatou, wanda dan asalin kasar Kamaru ne mai shekaru sittin da shida a duniya, ya ke rike da shugabancin hukumar ta CAF.

Yanzu haka kuma shi ne dan takara ba hamayya a zaben shugaban hukumar da za a gudanar a watan Maris mai zuwa.

A watan Satumba ne kuma aka amince da shawararsa ta haramta tsayawa ga kowa sai wadansu 'yan tsirarun na hannun damansa.

'Kawar da abokan adawa'

Masu sukar lamirinsa sun bayyana wannan mataki da cewa wata hanya ce ta kawar da abokan adawarsa daga takarar.

Jacques Anouma wani babban jami'i ne a Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, wanda ake ganin zai iya kalubalantar Hayatou.

Amma kuma a bisa tanade-tanaden kwaskwarimar da aka yiwa dokar takarar, mutane goma sha biyar din da ke Kwamitin Zartarwar CAF ne kawai za su iya tsayawa; kuma Anouma, wanda dan Ivory Coast ne, ba ya cikinsu.

Shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Liberia, Musa Bility, shi ne ya kalubalanci dokar a gaban Kotun ta Wasanni da ke Lausanne a kasar Switzerland, ya kuma ce sabon zubin ya yi hannun riga da tsarin dimokuradiyya kuma ba adalci a ciki:

"Babu yadda za a yi muna karni na ashirin da daya sannan mu rika kokarin jagorancin wasan kwallon kafa tamkar muna karni na goma sha takwas. Abin da ke faruwa a harkar shugabancin kwallon kafa a Afirka bai dace ba sam, kuma mun yi amanna muna da goyon baya a nahiyar".

Idan Kotun ta yanke shawarar soke sabuwar dokar to dama za ta bude ga kowa ya nemi darewa kujerar da ta fi ko wacce girma a harkar kwallon kafa a Afirka.

An shafa masa kashin kaji

Mutane da dama dai sun yi mamaki da Issa Hayatou, wanda ke fama da cutar koda, ya bayar da sanarwar cewa zai sake tsayawa takara.

Ga shi kuma an shafa masa kashin kaji sakamakon wadansu zarge-zarge na cin-hanci da rashawa.

A bara Kwamitin Gasar Olympic na Duniya, wanda shi mamba ne a cikinsa, ya kwabe shi saboda karbar na goro daga wani kamfani mai suna ISL, wanda tsohon abokin kasuwanci ne na FIFA.

Hayatou dai ya yi ikirarin cewa an yi amfani da kudin ne don bukukuwan cika shekaru arba'in da kafa hukumar CAF.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.