BBC navigation

Fitaccen Dan Wasan Burtaniya

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:24 GMT

'Yan wasan Olympics da na gasar Olympics ta nakasassu na Burtaniya ne suka kankane jerin sunayen 'yan wasan da aka ware don zabo wanda za a baiwa kyautar Fitaccen Dan Wasa na BBC a Shekarar 2012.

'Yan wasan tseren kekuna Bradley Wiggins da Sir Chris Hoy, da dan wasan tennis Andy Murray, da 'yan tsere Jessica Ennis da Mo Farah na cikin 'yan wasa goma sha biyun da sunayensu suka fito a cikin jerin.

Wadansu da sunayensu suka fito kuma su ne 'yar wasan tseren kwalekwale Katherine Garinger, da dan wasan golf Rory McIlroy, 'yar dambe Nicola Adams da sauransu.

'Yan wasan gasar Olympics ta nakasassu Sarah Storey, da Ellie Simmonds, da David Weir ma sunayensu sun fito a jerin wadanda ke sa ran samun kyautar wadda za a bayar ranar 16 ga watan Disamba.

Wadansu tsofaffin Fitattun 'Yan Wasan Burtaniya su uku na cikin alkalan da suka fitar da sunayen 'yan wasan goma sha biyu; kuma a ranar bayar da kyautar al'ummar kasar za su zabi daya daga ciki don ya zama Fitaccen Dan Wasan Burtaniya na bana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.