BBC navigation

An haramtawa Tevez tuka mota

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:00 GMT
Carlos Tevez

Carlos Tevez

An haramtawa dan wasan gaban Machester City, Carlos Tevez, tuka mota saboda kasa yin bayani lokacin da aka kama shi yana gudu fiye da kima a Lancashire.

Ranar 28 ga watan Maris ne dai 'yan sanda a garin Morecambe suka kama dan wasan saboda ketare awon gudun da doka ta kayyade.

Alkalai a Lancaster sun dora haramcin tuki na wucin gadi a kan Tevez; ana kuma sa ran watan Disamba za su ayyana tsawon lokacin da haramcin zai yi aiki.

Lauyan da ke kare dan wasan, Gwyn Lewis, ya shaida wa kotun cewa Tevez ya yarda cewa bai nunawa 'yan sanda takardunsa na shaida ba, laifin da kan jawo maki shida a ma'aunin lafuffukan tuki, kuma ka iya haddasa haramtawa mutum tuki kwata-kwata.

Sai dai kotun ta amince da rokon Mista Lewis cewa a dorawa dan wasan haramcin wucin-gadi har zuwa lokacin da za a kammala duba wani laifin na biyu na kasa nuna lasisinsa na tukin mota.

Ranar 15 ga watan Nuwamba ne aka kwace motar dan wasan kirar Porsche Panamera a Manchester lokacin da ya kasa nuna lasisinsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.