BBC navigation

Wace ce tawagar Afirka ta bana?

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:40 GMT
Tawagar Zambia lokacin da ta lashe Kofin Afirka

Tawagar Zambia lokacin da ta lashe Kofin Afirka

An fitar da sunayen zakarar Afirka, Zambia, da Ivory Coast, da Cape Verde, da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya don baiwa daya daga cikinsu kyautar Gwarzuwar Tawagar 'Yan Kwallon Afirka ta bana.

A watan Disamba ne dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, CAF, za ta sanar da kasar da ta yi nasarar zama gwarzuwa a nahiyar.

A watan Fabrariru ne dai Zambia ta ci Kofin Kasashen Afirka a karo na farko bayan da ta lallasa Ivory Coast a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a wasansu na karshe a Gabon.

Su kuwa Cape Verde da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2012 suka fara haskakawa, lokacin da Cape Verde ta cancanci shiga wata babbar gasa a karo na farko bayan ta casa Kamaru, wadda ta lashe kofin na Afirka har sau hudu.

Ita kuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi nasarar cancantar shiga Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ce a karo na farko sannan ta yi waje da Masar a wasan share fagen shiga Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.