BBC navigation

"Torres ya gama kure basirarsa"

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:58 GMT
Fernando Torres

Fernando Torres

Kocin riko na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Rafael Benitez ya ce a Liverpool Fernando Torres ya gama kure basirarsa.

Sabon kocin na Chelsea ya yi kira ga Torres ya yi kokari ya koma kan ganiyarsa tare da taimakon abokan wasansa.

Lokacin da yake buga wasa a Liverpool, Torres—dan shekara ashirin da takwas a duniya—ya ci kwallaye tamanin da daya a wasanni dari da arba'in da biyu, amma kwallaye goma sha tara kawai ya ci tun bayan komawarsa Chelsea a shekarar 2011.

"Basirar Torres yanzu ba ta kai lokacin da yake kan ganiyarsa ba, amma ina ganin zai iya sake komawa", inji Benitez.

Yayin da suke shirin karawa da Fulham ranar Laraba, 'yan wasan kungiyar ta Chelsea sun kasa cin ko daya daga cikin wasannin da suka buga guda biyar na baya-bayan nan a Gasar Premier.

Tsohon kocin na Liverpool ya kuma yi nuni da cewa mai yiwuwa ya sauya fasalin kungiyar ta yadda za ta kara karfi a baya saboda Chelsea na amfani da 'yan wasa goma sha tara ne kawai—kasa da yawan 'yan wasan da sauran kungiyoyi ke amfani da su.

A cewar Benitez, "Idan kana da dan wasan gaba to a koda yaushe za ka yi tunanin zai ci kwallo. Kuma idan kana da karfi a baya, to za ka iya kwace kwallo cikin sauki, za kuma ka fi samun damar cin kwallaye saboda za ka fi rike kwallo".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.