BBC navigation

Robson ta lashe kyautar WTA

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:26 GMT
Laura Robson

Laura Robson ta lashe kyautar sabuwar 'yar wasan tennis

An baiwa 'yar wasan tennis ta Birtaniya Laura Robson kyautar Hukumar Wasan Tennis ta Mata (WTA) ta sabuwar 'yar wasan tennis ta bana saboda bajintar da ta nuna a shekrar 2012.

Robson ta samu lambar azurfa a Gasar Olympics ta London 2012 a wasan 'yan bibbiyun da suka yi tare da Andy Murray, sannan kuma ta kai zagaye na hudu a gasar US Open bayan ta lallasa Kim Clijters da Li Na.

'Yar wasan mai shekaru goma sha takwas da haihuwa ce kuma 'yar Birtaniya ta farko a shekaru ashirin da biyu da ta kai wasan karshe a wata gasa da hukumar WTA ta shirya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.