BBC navigation

Za a soke Gasar Europa

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:09 GMT
Michel Platini

Michel Platini

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA, na tunanin soke Gasar Europa da kuma fadada Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta kunshi kungiyoyi sittin da hudu a maimakon talatin da biyu.

Shugaban UEFA, Michel Platini, ya shaidawa jaridar Ouest-France cewa: "Muna tattauna hakan. Za mu yanke shawara a 2014; amma ba abin da aka zartar tukunna".

Hakan dai na nufin kungiyoyin kwallon kafa na Ingila bakwai da na Scotland biyar ka iya shiga gasar a matakin share fage.

Hukumar ta UEFA tana tunanin sauya fasalin dukkanin gasar Turai ne daga 2015.

Platini ya kara da cewa: "Yanzu haka ana muhawara don fayyace irin fasalin da dukkanin gasar Turai za su dauka a tsakanin 2015 da 2018".

Idan aka fadada gasar ta Zakarun Turai ta kunshi kungiyoyi sittin da hudu, to kungiyoyin Ingila bakwai za su iya shiga a maimakon hudun da ke shiga yanzu haka, kuma yawan kungiyoyin Scotland a gasar ka iya karuwa zuwa biyar a maimakon biyun da ke shiga yanzu.

Wadansu dai na sukar lamirin Gasar Europa tun bayan da ta maye gurbin Gasar Cin Kofin UEFA a shekarar 2009, amma kuma Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta fi ta shahara.

A makon da ya gabata kocin Newcastle Alan Pardew ya ce Gasar Europa ta fi Gasar Zakarun Turai wuyar sha'ani saboda wasanninta sun fi yawa kuma a daren Alhamis.

Sai dai duk da haka kocin Tottenham Andre Villas-Boas—wanda ya yi nasarar lashe Gasar a 2011—ya ce ya kasa fahimtar dalilin da ya sa ake yi mata kallon gwale-gwale a Ingila.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.