BBC navigation

Frimpong ka iya bugawa Ghana

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:25 GMT
Emmanuel Frimpong

Emmanuel Frimpong

Dan wasan tsakiya Emmanuel Frimpong zai bugawa Ghana wasa yayin Gasar Cin Kofin Afirka ta 2013, bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta amince da sauyin kasar da ya yi.

Dan wasan mai shekaru ashirin da haihuwa, wanda kungiyar kwallon kafa ta Charlton ta karbo aronsa daga Arsenal, ya bugawa Ingila wasa a matakin 'yan kasa da shekaru goma sha shida, U-16, da kuma na 'yan kasa da shekaru goma sha bakwai, U-17.

FIFA ta ba shi dama ya bugawa kasarsa ta haihuwa ce bayan Hukumar Kwallon Kafa ta Scotland ta mika mata wata takarda da ke tabbatar da cewa Frimpong, wanda ke da tagwayen takardun shaidar zama dan kasa a Ghana da Burtaniya, bai buga wasa a wata gasa ba a makon da ya gabata.

Hakan dai na nufin yanzu za a iya sanya Frimpong a cikin tawagar Ghana a Gasar ta Cin Kofin Afirka wacce za a yi a Afirka ta Kudu badi.

Kuma burin Frimpong na tsawon shekaru biyu zai cika. Dan wasan dai ya ce: "Na sha fadi cewa, komai daren dadewa sai na bugawa Ghana kwallo, saboda na yi imani ni dan Ghana ne".

Ya kuma kara da cewa: "Ni da iyali na mun ci moriyar Ingila sosai da sosai, amma a karshe ba zai yiwu in bugawa Ingila ba, saboda ni ba baturen Ingila ba ne--ni dan Ghana ne".

Sai dai kuma Frimpong zai fuskanci jan aiki neman gurbi a tawagar Ghana a karkashin jagorancin Kwesi Appiah, saboda tunanin da ake yi cewa ba wanda ya kai 'yan wasan tsakiyar tawagar kwarewa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.