BBC navigation

Golf: Haramta dogayen sanduna

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 21:06 GMT
Peter Dawson

Shugaban kungiyar golf ta R&A, Peter Dawson

Hukumomin kula da wasan golf na duniya suna shawarar takaita amfani da sandunan golf masu tsawo.

Sannan kuma za a haramtawa 'yan wasan golf dogara sandunan a kirji ko a ciki idan za su buga kwallo daga shekarar 2016.

'Yan wasan da suka yi amfani da sanduna masu tsawo ne dai suka lashe manya-manyan wasannin golf biyar da suka gabata; amma kungiyar Royal & Ancient Club (R&A) da ke Scotland da kuma Hukumar Wasan Golf ta Amurka sun ce da sake.

Shugaban kungiyar R&A Peter Dawson ya ce: "Abin da ke damunmu shi ne bugun kwallo da sandar da aka jingina a jiki na neman maye gurbin bugun da muka sani na al'ada".

Za a kyale a ci gaba da amfani da sandunan da aka kara musu tsawo amma dole ne a rika nesanta su da jiki.

Duk wanda ya karya wannan doka dai za a hukunta shi ta hanyar sanya shi ya sarayar da rami daya a wasa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.