BBC navigation

Za mu daga Kofin Duniya —Roy

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 21:42 GMT
Roy Hodgson

Kocin Ingila, Roy Hodgson, ya ce yaransa na da damar daga Kofin Duniya

Kocin tawagar kwallon kafa ta Ingila, Roy Hodgson, ya ce 'yan wasansa na da kyakkyawar dama ta daga Kofin Duniya na 2014 in har suka samu shiga gasar wadda za a buga a Brazil.

Yanzu haka dai tawagar ta Ingila ce a matsayi na hudu a rukunin da take na neman gurbin zuwa gasar bayan da ta buga wasanni hudu.

Hodgson na wata ziyara a Brazil don duba wuraren da tawagar ta Ingila za ta rika atisaye a shekarar ta 2014.

Ya shaidawa BBC cewa: "In har muka samu zuwa nan za mu yi amanna muna da kyakkyawar dama".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.