BBC navigation

Wanene zai lashe Ballon d'Or?

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:12 GMT

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta bayyana sunayen Lionel Messi, da Cristiano Ronaldo, da Andres Iniesta a matsayin 'yan wasan kwallon kafa ukun da za a baiwa daya daga cikinsu kyautar gwarzon kwallon kafa ta Ballon d'Or.

Dan shekaru ashirin da biyar da haihuwa, Messi ya ci kwallaye tamanin da biyu a bana—wato ke nan saura uku ya kamo Gerd Mueller, wanda adadin kwallayen da ya ci a 1972 ya fi na kowa a tarihin kwallo.

Shi ma dan wasan Real Madrid, kuma tsohon dan wasan Manchester United, Ronaldo, sunansa ya samu shiga; haka ma dan wasan Barcelona, Iniesta.

An kuma ware sunayen Pep Guardiola, da Vicente del Bosque, da Jose Mourinho, don baiwa daya daga cikinsu kyautar gwarzon koci na bana.

Ranar 7 ga watan Janairu za a sanar da sunayen wadanda suka yi nasara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.